TARIHIN SHEHU TIJJANI (R.A)
SON SHEHU SAI DANGATA
DAGA BAKIN
SAYADI MUSA NA ANNABI
DATE:14-11-2018/06-03-1440
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته
الحمدلله واسع الكرم والجود والصلاة والسلام علي سيدنا محمد الموصوف بالكرم والجود وعلى اله وصحبه وسلم
TARIHIN MAULANA SHEHU AHMAD TIJJANI RTA
Nasabar Shehu Tijjani Rta
Shine Maulana Ahmad tijjani Dan Muhammad Dan Mukhtar Dan Ahmad Dan Muhammad Dan Salim Dan Eid Dan Salim Dan Ahmad Dan Aliyu Dan Abdullah Dan Abbas Dan Abduljabbar Dan Idris Dan Ishaq Dan Aliyu Zainul Abidin Dan Ahmad Dan Muhammad Dan Hasanul Muthanna Dan Dan Hasan Jikan Shugaba Saw Dan Sayd Aliyu Dan Sayda Fadima A.s Yar Shugaba Saw
An Haifi Maulana Shehu Tijjani Rta A Shekarar 1150 Bayan Hijira A Garin Ainu MADHI,Ya Kuma Rayu A Cikin ta Cikin tsantsar kulawa,Abin kiyayewa Da Kiyayewar Allah.
Ya Haddace Alqurani Tun Yana Da Shekaru 7 Hadda Mai Kyau,Ya Kuma Haddace Alquranin ne Da Ruwayar WARSHU.
Bayan Ya Haddace Alquranin Sai Ya Shagala da Neman Ilimi.
Ya Karanci Littafin MUKHTASARUL KHALIL A Wajan Shehin sa Sayd Mabruk Ibn Afiya Rta Tare Da Ahlari Da Ibn Rushd.
Sannan Ya Cigaba Cikin Neman Ragowar Iliman A Cikin Garin su
Shehu Tijjani Rta Ya karanci Duk Wani Fanni da Ake nema Cikin Addinin Musulunci,Sai Da yakai Malamai Nagarin su Suna Amfanuwa Da Fatawar sa.
Sannan Shehu Tijjani Rta Ya Zama BAHARU Cikin Ilimin Addinin Musulunci Sai Ya Kutsa Cikin Ilimin Sufanci,Maana Neman Yardar Allah Da Maarifar Sa.A Wannan Fannin Sai Da Shehu Tijjani Rta Ya Zama Kogin Da Bashi da Gefe,Domin Sai da Takai Babu Wani Waliyyi Da Ya Samu Irin Ilimin da Shehu Tijjani Rta Yake Dauke Dashi.
Mas'ala Idan ta Rikicewa Malaman Duniya Daga Ko Ina Kawowa Ake Ga Shehu Tijjani Rta,Domin Ana Zuwa Zaa Samu Karin Ilimi Akan Fatawar Da Aka zo Masa Da Ita,Domin Shehu Tijjani Rta Baa Wiliya Ba A Ilimin ma Shi MAKTUM Ne
A Ilimin Sharia Shehu Tijjani Rta MAKTUM Ne A Ilimin Sufanci MAKTUM Ne,A Bangaren Mu'amala da Halitta Babu Irin sa Cikin Waliyyai,A Bangaren Kasuwanci Tare da Mu'amala da Abokan sa nan ma Daban Yake,Ta ko ina ka biyo Shehu Tijjani Rta Daban Yake.
Amma Yan Uwa Zamu Gane Hakan Idan Muka Kutsa Cikin Tarihin Shehu Tijjani Rta Ta kowane Bangare.
Domin Tarihin Shehu Tijjani Rta Ba Tarihi ne Da Zaayi Shi a Wannan Gidan kadan ba,Aa Tarihi ne da ya kamata A yi shi Sosai,Domin Muma A Akanmu Mu Bawa Kanmu Amsa Da Cewa
INA YA KAMAR KA TIJJANI
INA SO IN JI ZANCEN KA...NAAM YA SHEHU TIJJANI
Alhamdulillah Zamu tsaya Anan Sai kuma Wani Satin
Fatiha Da Salatal Fatih Hadiyya Ga Shehu Tijjani Rta
Alhamdulillah
❤
An bude wannan shafin na yanar gizo saboda yada soyayyar Manzon Allah S.A.W ta hanyar watsa wakokin yabon Manzon Allah S.A.W wato qasida wanda sha'irai mawaka Manzon Allah S.A.W sukeyi saboda kaunar su da masoyin su wato shugaban farko da karshe sayyadil wujudi S.A.W Allah ya qara mana soyayyar Manzon Allah S.A.W Ameeeeeeeeeeeeeeeen........
Wednesday, November 14, 2018
HAPPY MAULUD
Subscribe to:
Posts (Atom)
QASIDU
-
TARIHIN SHEHU TIJJANI (R.A) SON SHEHU SAI DANGATA DAGA BAKIN SAYADI MUSA NA ANNABI DATE:14-11-2018/06-03-1440 السلام عليكم ور...
-
An bude wannan shafin na yanar gizo saboda yada soyayyar Manzon Allah S.A.W ta hanyar watsa wakokin yabon Manzon Allah S.A.W wato qasida w...